Dangane da tabbatar da tsaro,a yayin gudanar da zabukan kansiloli da ciyamomin na babban birnin tarayya Abuja, rundunar yan sanda na babban birnin tarayya, a yau alhamis ne ta ba da sanarwar cewa,zata takaita zirga -zirga daga karfe 12 na daren jumma’a 11 ga watan faburairu zuwa yammacin asabar karfe hudun 12 ga watan faburairun 2022,domin Kammala zaben.
Sai dai dokar ta haramtawa daliban da zasu zana jarabawar WAEC a duk fadin kasar,har da ma sauran ma’aikata masu mahimmanci.
A wata sanarwa,jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda reshen babban birnin tarayya, DSP Josephine Adeh,tayi gargadin cewa,wadan da basu shiga cikin nau’o’in da aka lissafa ba,su bi dokar da aka gindaya,ko su fuskanci fushin shari’a.
DSP Adeh ta kara da cewa,rundunar yan sandan,a kokarinta na inganta tsaro zata tura sojoji zuwa zaben kananan hukumomin yankin da za a gudanar a ranar 12 ga watan Faburairu 2022.kuma zata yi abinda ya dace don tabbatar da tsaro da kuma aiwatar da dokar da ta ayyana a ranar zaben.
Ta kara da cewa,takunkumin da ya kunno kai tsakanin karfe 12 na daren jumma’an,an sanya shi ne domin baiwa yan sanda damar yin hadin gwiwa tare da sauran hukumomin tsaro domin gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.
Kwamishinan yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, CP Babaji Sunday, yayin da yake nuna amincewar sa ga matakan tsaro da aka riga aka dauka,ya bukaci jama’an babban birnin da su fito su yi anfani da ‘yancin su na kada kuri’a ba tare da tsoron tsangwama ko cin zarafi ba.
Duk da haka ya lura cewa,wannan dokar ta shafi ma’aikata masu mahimmanci da kuma daliban da aka tsara kwatsam don rubuta jarabawar WAEC a duk fadin kasar.
Yana mai jaddada cewa duk bangarorin da aka samu da akasin bin doka za su fuskanci fushin doka.
By Fatima Abubakar