Yan okada sun sake kai hari a same Global Estate a gundumar Galadimawa yayin da wata mota ta kashe yan babur din mutum biyu

0
20

Masu tuka babura sama da 100 sun kai hari a Same Global Estate dake unguwar Dakwo ta gundumar Galadimawa a Abuja domin daukar fansar mutuwar abokanan aikinsu mutum biyu.

Lamarin ya faru ne bayan da aka ruwaito wani direban mota ya bugi mahaya Okadan a ranar Lahadin ta yau kuma ya garzaya cikin Estate din domin tsira.

Mun samu rahoton cewa mahayan Okadan sun kona gine-gine biyu a cikin gidan.

Mazauna unguwar sun shaida wa wakilinmu cewa, masu tuka baburan sun kai farmaki gidan ne a yunkurinsu na cafke wani direban mota da ba a san ko su waye ba.

Sun yi nuni da cewa, dimbin babura ne suka fatattaki direban motar bayan da lamarin ya faru.

Manajan Estate, Mista Adebisi Adelowo, da yake magana kan lamarin ya ce, “Sama da mahayan babura 100  ne suka kai hari a rukuninmu a sa’o’i da suka wuce. Sun yi kokarin kona gidan ta hanyar kona gine-gine biyu.

“Sun ja kofar mu suka fara jifan gidajen mutane. Ba mu iya hana su ba har sai da ‘yan sanda da sojoji suka shiga tsakani.

“Daga baya mun samu labarin cewa sun kai harin ne a kan wasu abokan aikinsu guda biyu da wani direban mota ya kashe inda ya ruga da gudu  domin tsira da ransa yayin da aka bi shi da manyan duwatsu da wasu muggan makamai.

“Matukin wanda ba mazaunin gidan namu ba ne ya ruga cikin gidan ne saboda ya lura da ofishin ‘yan sanda a gaban gidan.

By Fatima Abubakar