Tinubu zai gana da Gwamnonin APC gabanin neman abokin mataimakin sa

0
48
  • A ranar Laraba ne da ya gabata dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu, da takwaransa na jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, suka fara neman abokan takararsu.

Kakakin kungiyar kamfen din Tinubu, Mista Bayo Onanuga, a wata hira da ya yi da daya daga cikin wakilanmu, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zai gana da gwamnonin APC da ya ce za su zabi abokin takarar tsohon gwamnan jihar Legas.

An kuma tattaro cewa Tinubu zai gana da shugabannin jam’iyyar da suka hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, kafin karshen mako.

Yayin da Tinubu ya fara neman abokin takararsa, a ranar Laraba Atiku ya yi wata ganawar sirri da gwamnonin PDP a Abuja da nufin zabar dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar.

A zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da aka fara tun ranar Talata kuma aka zagaye shi a ranar Laraba, Tinubu ya samu kuri’u 1,271 domin samun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Shugaban kwamitin gudanar da zaben gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi a dandalin Eagle Square da ke Abuja ya bayyana cewa tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi ya samu kuri’u 316; mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, kuri’u 235; wani tsohon karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba, kuri’a daya; Sanata Rochas Okorocha da Fasto Tunde Bakare ba su samu kuri’u ko daya ba.

A ranar Litinin ne gwamnonin Arewa suka dage kan cewa za a sauya madafun iko zuwa Kudu duk da amincewar da shugaban majalisar dattawa na kasa Ahmad Lawan daga yankin Arewa maso Gabas ya yi a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Daga Fatima Abubakar