Mata mu kula:Shin ko kunsan cewa rashin aske gashin gaba bayan al’ada yana jawo warin jiki.

0
1023
beauty cartoon woman do epilator before and after

Kakannin mu da iyayenmu ba su iya zama da mu su tattauna akan gashin da ke al’auranmu, amma zamu iya cewa muna godiya ga kafofin watsa labarai da intanet,domin ko mu ‘yan mata yana taimaka mana wajen bincike, muhawara, da kuma nazarin zabin mu kan yadda za mu iya gyara jikinmu musamman ga wajajen da suke kawo mana wari.

Da yawanmu akwai tambayoyin da yake wakana akanmu game da aske gashin al’aura da kuma barinsa

 

Shin gashin gaba yana da wata manufa?

 

Shin akwai wasu fa’idodin kiwon lafiya da ke tattare da su?

 

Za mu iya askewa? Za a iya samun illa bayan askewa?

Wadda anan zamuyi kokarin fahimtar da ku fahimtar menene gashin al’aura da fa’ida da rashin aske shi aske shi musamman bayan an gama al’ada.

A bisa bincike an nuna cewa gashin gaba yana nuna alamar balaga da kuma zama garkuwar kariya daga farji, haka zalika a yayin da mace ta fara fitarda irin wannan gashi ne ake fara tsammanta mata al’ada nata ya kusa. Mun san cewa jinin al’ada ya kasance abune mafi kyamata domin ya kasance yanada karni wadda ko ga ita mace alokacin da take fitarda shi bata son kallonsa. A bisa bincike, an nuna cewa alokacin da mace take al’ada nata gashin dake farjinta yana iya mannewa da wannan jinin ta yadda ko da ta wanke bazai iya fita duka ba.

Da wannan ne yasa in har ta gama batayi aski ba zai iya janyo mata wari da har zai iya bata mata kwalliya, wanda duk saka kayanta da kwalliyanta zai kasance bai biya kudin sabulu ba.

Don haka ya kasance wajibi a gare mu mata askin gashin da baa so na jiki ya zama wajibi domin kuwa shi ne abu mafi kankani da zai iya bata mana kwalliya duk saka turarenmu sai ya zaman a banza kuma ya zama yana iya jawo mana tsana da hantara a ciki al’umma.

BY: UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.