HANYOYIN DA ZAMU BI WAJEN CIRE WARIN BAKI

0
53

 Abune da zamubi mafi sauki wajen inganta numfashin da muke shaka, tare da inganta hakoranmu da kuma karawa dasorinmu lafiya da karko. Warin baki abune mafi muni da yake ruguza mana kwalliya, domin kuwa duk yadda ka kai ga caba ado idan har bakinka ya kasance da wari yana zubar da daraja da kimanka wajen jama’a. don haka yau na kawo muku hanyoyi da matakai da zamubi wajen ganin mun kaucewa wanda matsala dake kawo mana cikas a kwalliyanmu.

 

  1. Yawaita goge hakori da wankewa akai akai

dasorinmu wanda yake kasan hakro, yana tattara ƙwayoyin cuta masu haifar da warin baki, wadda yawancin Abincin da mukeci yana makalewa ta wajen tsakanin hakori saboda haka ne yake kara matsalar warin baki. Don haka yakasance muna goge haƙoran mu aƙalla sau biyu kowace rana, kuma mu kasance muna tsakale hakoranmu duk sanda muka gama cin abinci.

  1. Kurkure baki.

kurkure baki yana kara kariya tare da  kawar da kwayoyin cuta ga bakinmu. Haka kuma zaku iya amfani da abubuwan kurkure baki masu ɗanɗanon minty mai kamshi wanda zai sa ku ji daɗi. Amma ku tabbatar kayan wanke bakin da ku zaba yana kashe kwayoyin cuta masu haifar da warin baki. Amma mafi muhimmanci shine Kurkure wa kullun tare da wanke wa da abubuwa masu karko.

  1. Yawaita wanke harshe a kullum.

Dan fari fari da ake samu akan harshe yana iya zama masaukin kwayoyin cuta masu saka warin baki, don haka goge harshe a kullum na kawar da wannan kwayoyin cutan. Haka zalika mu kasance a koda yaushe muna kula wajen gogewa domin kuwa in har ana yiwa harshe amfani da brush masu karfi zai iya illata harshe.

  1. A guji abinci masu sanya warin baki.

Cin Albasa da tafarnuwa manyan laifuka ne ga masu matsalan warin baki, domin kuwa kunsa mutane sun kasu kasha da yawa akwai wanda in har suka ci da zarar sunyi brush zai fita, akwai wanda kuma yana daukan kwana da kwanaki kafun ya fita daga bakinsu. Toh in har kasan kanada wannan matsala kauracewa danyen albasa da tafarnuwa shi ne mafi sauki da zai kawar maka da warin baki. Haka kuma in har ya kama dole a ci toh a tabbata ba’a je wajen aiki ko kuma wajen abokai ba.

  1. Kauracewa shan Sigari.

Ban da haifar da ciwon daji, shan taba na iya lalatamana dasori, yana kuma bata haƙoranmu, kuma yana kara matsalan warin baki. Don haka idan har mai matsalan warin baki yana shan sigari toh sai ya tabbata ya daina kafun zai samu matsalar ta warware.

  1. Kauracewa shan kayan zaki bayan cin abincin dare.

Kwayoyin cutan dake cikin bakinmu suna son zaki, wanda yana lalata mana hakora kuma yana sa warin baki. Don haka mu kasance muna cin cin gam din da bashida zaki in harm un gama cin abinci.

  1. Yawaita shan ruwa akai akai

Shan ruwa shi ne abu mafi muhimmanci wajen inganta lafiyan jikinmu musamman ma ga kwalliyar mu, haka zalika bias binciken da likitoci suka gudanar yawaita shan ruwa yana kara taimakawa wajen rage warin baki. Don haka idan kun kasance kuna cikin wannan matsala ku yawaita shan ruwa.

  1. Yawaita tuntuban likita a koda yaushe.

Idan har aka yi amfani da waennan hanyoyi amma matsalar bata kau ba to a gaggauta wajen tuntuban likita domin yana shi ne abu mafi muhimmanci ga lafiyarmu. 

 

BY: UMMU KHULTHUM ABDULKADIR