Kalar jan bakin da mace mai duhu zatayi amfani dashi suna da yawa kuma sun kasance masu kyau kaman yadda masu shafa su suke da kyau, kuma kaman na fararen mata. Mata masu duhu sun kasance suna wahala wajen ganin sun zabi jan baki da zai fito dasu ya kuma musu kyau a fuska, wadda shi jan baki ya kasance abu mafi sauki wajen kara fito ma mace da kalar fatanta da kuma kyawun fuskanta,in har kin kasance cikin mata masu duhun da suke damuwa wajen zaban janbaki da zai dace da kalar fatansu a ynxu na kawo miki wasu hanyoyi da zakibi wajen kin cimma burinki. Tabbas nasan cewa zaban kalar janbaki nada wahala musamman ga mata masu fata mai duhu domin da zarar baki zaba kalar da ya dace ba toh kin bata kwalliyarki.
Musamman mu mata abunda yafi damun mu wajen kwalliya shi ne yanayin kalar fatanmu har ma ga fararen matan, duk sanda mace tazo zaban kalar janbaki toh damuwanta shi ne ta yaya zan zabi jan baki da zai fito mun da kyawun fuska na? mata da suke da fata mai duhu zasu iya shafa janbaki mai kalar daukan idanu wadda zai yi over powering na fararen mata. Amma kuma zaki iya duba da waje da kuma taron da zakije kafun zabar kala mai dauke ido.
Jan baki mafi kyau da zai kara fito da kyawun mace mai duhu sun hada da jan baki mai launin nude color wato kalar hoda kenan, jan baki mai launin nude yana karawa mace mai duhu kyau musamman idan ta zagaye lebenta da bronze wato gazal da tayi ja gira dashi sai tazo ta shafa kalar nude a tsakiya yana matukar kawata mata fuska. Haka kuma kalar royal peach shima yana matukar kara fito da kyawun mace mai duhu shima musamman zane lebenta da gazal din jagira tazo ta shafa royal peach a tsakiya.haka kuma kalar chocolate shima yana saka mace mai duhu kara mata kyau. Da karshe kuma mai zalla wadda ba kala a ciki shima yana matukar kara fito da mace mai duhu domin yana kara haska mata fuska.
BY: UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.