Hukumar kiyaye hadurra ta tarayya ta tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu shida a wasu hadurran mota guda uku da suka afku a kan hanyar Gombe zuwa unguwar Pantami ranar Juma’a.
Kwamandan rundunar FRSC reshen jihar Gombe Felix Theman ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a ranar Asabar.
Theman ya ce, abubuwan da ake zargin sun haddasa hadurran da suka hada da babbar mota daya, karama daya da babur daya ya wuce gona da iri, da gudu da motoci ke yi.
Ya bayyana cewa wadanda suka samu raunuka daban-daban an kai su asibitoci domin kula da lafiyarsu tare da kai gawarwakin zuwa dakin ajiyar gawarwaki.
Theman ya yi nuni da cewa, hadurran sun afku ne a yankunan da ke da yawan jama’a tare da yin kasadar hasarar rayuka.
Kwamandan ya ce, a daya daga cikin hadurran, wani direban babur ne ya goyo fasinjoji uku, inda ya ce hakan ba abu ne da za a amince da shi ba, domin jami’an na wayar da kan su amma wasu ba su ji ba.
Theman ya ce, za a tura karin motocin sintiri da jami’an tsaro zuwa wuraren da ke daukar jerin hadurruka.
- Daga Fatima Abubakar.