Shugaba muhammadu Buhari ya kaddamar da kasuwar sabon gari da kuma hanyoyi a zaria.

0
308

A yau ne jumu’a 21 ga watan janairu 2022 shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da bukin bude babbar kasuwar zamani da kuma hanyoyi a Zaria, karamar hukumar sabon gari ta jahar Kaduna.

Kasuwar sabon garin wanda take dauke da shaguna 2762 da ofisoshin masu gudanarwa da wurin killace motoci, hukumar kashe gobara, ofisoshin matakan tsaro da sauransu.

Shugaban ya kaddamarda rukuni daya da na biyu na kasuwan wanda ana ci gaba da aiki a rukuni na uku.

Bugu da kari hanyoyin da ya kaddamar a sabon garin suna karkashin sababbin ayyukan hukumar kula da birane.

Gwamna Nasiru Elrufa’i ya jagoranci Buhari da sauran ministoci zuwa fadar mai martaba sarkin zazzau Alh. Ahmad Bamalli kana daga nan suka wuce Kaduna.

A jiya ne shugaban ya sauka a Kaduna domin kaddamar da aiki na kwana biyu.

By Fatima Abubakar.