A dare daya Allah kanyi bature: rayuwan masu kama kifi a yemen ya sauya bayan gamuwa da aman kifin whale da ya kai kimanin Rs 10 crore

0
268

Ba ko wane keda matsaniya akan tsadan amman kifin whale ba, tabbas aman kifin yana da tarin albarkatu masu tsada.

Wasu masu kama kifi a yemen sunyi karo da makuddan dukiya da yafi kimanin Rs 10 crore ajikin mattacen kifin whale.

Kasar yemen na daya daga cikin kasa mafi talauci a duniya sun Dogara ne da kama kifi wajan samun abinci.

Sun samu wani abu da ake kira ambagris wadda baki ne kuma ana samun shi ne acikin hanjin babban kifin whales.

Wani mai kama kifi daga seriah ne ya fara sanar da wasu talatin da biyar [35] a Gulf of Aden game da wanan mattaccen kifin, ya kuma sanar dasu cewa zasu iya samun ambagris. A lokacin da masu kama kifin su ka gan kifin sun san cewa akwai abu a cikin kifin.

Sai suka jawo kifin har izuwa bakin ruwan, bayan yanyanka kifin ne sukayi gamo da bakin ambergris kg 127.

“Abune da bamu taba tunanin ba, dukan mu talaka ne. bamu taba tsammanin wannan abun zai kawo mana wannan yawan dukiyan ba,” daya daga cikin masu kama kifin ya fadawa BBC.

Shi de Ambergris ana kiransa albarkatun teku ko kuma zinari mai tasowa akan ruwa.yana daga cikin abubuwa da aka fi nima domin kuwa ana amfani dashi wajan hada turare domin sashi ya dade idan akayi amfani dashi. Kowani kilogram na ambargriscan ana saiyar das hi dala dubu hamsin ($50,000)

Masu kama kifin sun sayar dashi akan biliyan 1.3 a kudin yemen wadda yaje daidai da dalla million 1.5 watto (Rs 10.96 crore) ga wani dan kasuwa daga united arab emirate. Sun raba kudin daidai kuma suka raba wasu kudin zuwa ga talakawa a angwanin su.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho