Mashed potatoes

0
394

Mashed potatoes abinci ne da yake da saukin hadawa kuma baya bukatan abubuwa hadawa masu yawa ko tsada, yawanci  abubuwan da ake hada shi das u abu ne wadda amarya da uwargida ba zasu rasa ba a cikin kitchen insu.

Shi wannan abincin baya daukan lokaci ga daddi ga kuma rike ciki.

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

  • Dankalin turawa
  • Narkakken butter
  • Gishiri
  • Masoro
  • Tafarnuwa
  • Madaran ruwa

YADDA AKE HADA MASHED POTATOES

  1. Zamu fere dankalin mu sai mu yanka shi biyu daga tsakiya, daga nan mu sa a cikin ruwan da muka sa gishiri.
  2. Mu daura a wuta mu barshi yayi tausa kuma ya dahu ta yadda cokali mai yatsu watto fork zai iyya shiga ciki. Sai mu tsame a matsama.     
  3. Sai mu daura madaran ruwan mu a wuta ya danyi zafi, ba zafi sosai ba ya danyi lab- lab.
  4. Mu zuba dankalin mu daya dahu a kwanu sai mu sa butter a ciki mu motsa watto mashing. Sa’anan mu dinga sa madaran mu kadan-kadan muna motsawa da potato masher har sai komai ya hadu sosai.       
  5. Sai mu sa gishiri da tafarnuwa da masoro mu motsa. Toh mashed potatoes inmu ya hadu aci lafiya.

Rubutawa:Firdausi Musa Dantsoho