Yadda Ake Hadda Mince Meat Sandwiches

0
1048

A yau zamu hadda sandwich ne amma na nikkakken nama. Shi sandwich ana amfani ne da bredi wajan hadda shi. Wasu na amfani da kaza wasu kifi wasu zalan ganye watto lattuce wajan hadda sandwich amma mu nama zamuyi anfani dashi.

Abubuwan Bukata Sune:

  • Bredi slice
  • Nikakken nama
  • Tumatir mai karfi
  • Ketchup
  • Bama
  • Lettuce
  • Sinadarin dandano da kamshi

Yadda Ake Haddawa

  1. Zamu daura tukunyan suyan mu mai tsafta a wuta, sai mu sa mai kadan, mu zuba nikakken naman mu da albasa da sinadaran dandano da na kamshi mu dinga juyawa har naman mu ya dahu.
  2. A cikin kwano mai tsafta mu zuba bama, ketchup da dan sinadarin dandano mu gauraya ya hadu.                                                               
  3. Sai mu samu slice bread inmu guda biyu mu shafa hadin bama mu sai mu zuba nikakken naman mu akai, sai mu daura lettuce, sai mu daura yankakken tumatir sai mu rufe da wanni bredin.
  4. Haka zamuyi wa duka bredin, sai mu dauko bredin mu gasa a tukunyan gashin mu ko toaster ko non stick frying pan.
  5. Bayan bredin ya gasu toh mince meat sandwich inmu ya hadu aci lafiya.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho