Abun mamaki Wata mata ta kashe mijinta da wuka saboda kishi  a jihar Nasarawa

0
533

 

Wata matar aure mai suna Atika ta daba wa mijinta wuka har lahira a kan matarsa ​​ta biyu a Angwa Yerima da ke Mararaba a karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

An tattaro cewa marigayin, Ibrahim Ahmad Salihu, mai shekaru 37, ya kasance yana kwana biyu tare da kowanne daga cikin matansa guda biyu a jere kuma yana da dabi’ar bankwana da kowanne daga cikinsu a duk lokacin da zai tafi dakin dayan.

 A ranar Asabar da daddare ne aka ce Ibrahim ya tafi dakin Atika, wacce ita ce matarsa ​​ta farko, domin yi mata bankwana kuma ya tafi dakin mata ta biyu da ke cikin gidan.

“Kuma abin da ya yi ke nan a ranar da misalin karfe 8 na dare, sai kawai Atika ta amsa a fusace ta ciji yatsar sa,” inji wata majiya daga cikin harabar gidan.

 Da take zantawa da jaridar daily trust , mahaifiyar marigayiyar, Hajiya Hauwa Umar, ta ce wanda ake zargin ta daba wa danta wuka ne yayin da matarsa ta biyu ke kokarin yi gyara masa raunin da ya ji.

“Dayan matars ta garzaya domin ceto shi tana kokarin daure dan yatsan da abin ya shafa, amma matar ta farko, wacce ta riga ta kulle kofar gidan, ta rike shi daga baya ta caka masa wuka a wuya akai akai ba tare da ta sau sauta ba.”

An tabbatar da mutuwar Ibrahim a asibitin kuma an yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, yayin da aka ce wanda ake zargin tana hannun ‘yan sanda.

Makwabcin ma’auratan, Audu Gambo Akor ya yi ikirarin cewa suna tafka muhawara kan shirin da marigayin ya Ke yi na rabuwa da Atika.

 “Wannan wahala ta Dade Tana faruwa, saboda mutumin ya so ya sake ta kwana daya kafin lamarin ya faru amma mahaifiyarsa ta sa baki.”  Akor yace.

 

By: Firdausi Musa Dantsoho