Yadda ake hada yoghurt a gida

0
1831

Yoghurt sanannen abinci ne kuma mai gina jiki, wanda ba kawai yana da sauƙi ba ne kuma ya dace a ci  yana da daɗi sosai.

Yin yoghurt a gida yana da sauƙi, baya buƙatar amfani da abun hadda Yogurt, Crock-pot, ko Instant Pot.

 Iya abin da kuke buƙata shine sinadarai guda biyu: cikakkiyar madara mai inganci da yoghurt ɗin da aka yi ko siya.

 Yin yoghurt a gida zai ba da damar dangin ku duka su ji daɗin fa’idodin kiwon lafiya da ɗanɗano mai ɗadi na yogurt.

Yin yoghurt yana da sauƙi kuma yana da saukin sha.  Yawancin  yoghurt ya dogara ne akan kayan farawa watto starter, kayan farawan shine yoghurt wanda aka riga aka hada (yawanci ana saya) shi wannan starter  in ana saka shi a cikin madara da aka tafasa a bar shi ya zama yoghurt.

 

Don hadda Yoghurt daga farko, kuna buƙatar:

 

  • 1-3 lita na madara

 

  • Jakar starter culture ko karamar cokali 2 na yogurt mara siga 
  • Ya kamata adadin madarar da aka ƙara ya kasance ƙarƙashin adadin yoghurt da za ku samu a ƙarshe.

 Yadda ake hadda yoghurt

  1. Da fari dai, sai kizuba madararki a cikin babban tukunya a barshi har sai ya fara tafasa a ci gaba da motsa shi don kada ya kone.
  2. Na biyu,  a sauke madara daga wuta a ba shi damar yin sanyi zuwa kusan 40 ° C.  Yi amfani da ma’aunin zafi  sai ku sanya hannun ku ciki domin tabbatar da cewa yana da dumi kuma ba shi da zafi sosai da zai kone ki.
  3. Na uku, saka yoghurt Mara siga a cikin madaran  mai dumi kuma a gayyata kayan haɗin har sai sun hade a cikin madarar.
  4. Na hudu, dafa kwantena na yogurt  inki da ruwan zãfi kafin a zuba duka yogurt in da aka cakuda da madara a cikin kwantena.
  1. Bayan haka, sai asa kwantenan a cikin wuri mai dumi ko a rufe shi da barguna don kasancewa cikin zafin.  A bar shi na aƙalla awanni 8 sannan, a duba yogurt ɗin  don tabbatar da ya yi kauri.

  1. Daga karshe ki bar yoghurt dinki ya zauna a cikin firij domin yayi kauri, daga nan zaku iya zuba masa siga, zuma ko ki cin shi yadda yake.

Yoghurt na gida zai iya ɗaukar har zuwa kwanaki uku a cikin firiji ba tare da ya lallace ba.

By: Firdausi Musa Dantsoho