YADDA AKE HADA LEMUN VIRGIN STRAWBERRY PINA COLADA

0
374

Wannan lemun haddiyar lemu ce wadda ake hada ta da strawberry,abarba,madaran kwakwa.Yana da saukin hadawa kuma yana da daddin sha.

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

 • Abarba mai kankara
 • Strawberry mai kankara
 • Madaram ruwa
 • Sigar
 • Madaran kwakwa (coconut milk)
 • Lemun zaki
 • Lemun tsami
 • Vanilla extract
 • Kankara (ice cubes)

YADDA AKE HADA LEMUN:

 1. Da farko zamu samu blendan mu mai karfi wadda zai iya markade kankara tabbatar abun markaden mu watto blender in yana da kyau da karfin da zai markade.
 2. Sai mu zuba abarban mu wadda muka yanka kanana yayyi kankara acikin abun markade(blender).                               
 3. Zamu dauko strawberry inmu mai kankara mu sa a ciki, sai mu sa lemun tsami, vanilla flavor,sugar, madara, lemun zaki,madaran kwakwa da kankara duk a ciki mu markade.
 4. Bayan mun markade ya markadu toh lemun strawberry pina coladan mu ya hadu.

 

By: Firdausi Musa Dantsoho