Kasar Saudiyya ta bayyana 11 ga watan Maris a matsayin 1 ga watan Ramadan.

0
34

Kasar Saudiyya ta bayyana 11 ga watan Maris a matsayin 1 ga watan Ramadan

 

Kwamitin Ganin Wata a ƙasar Saudiyya ya Sanar da Ganin Jinjirin Watan Azumin Ramadan na shekarar 1445 bayan hijirar Annabi Muhammad (S.A.W).
Saudiyya ta Sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Harami na Facebook, wanda Hakan ke nufin watan Sha’aban yazo karshe a Kwanaki 29 kenan. Inda Ramadan zai fara a gobe Litinin a ƙasar.

Ibadar Azumi dai na cikin Rukunan Musulunci guda Biyar, musulman Duniya dai na shafe Kwanaki 30 ko 29 suna gudanar da Azumin.

Kuma dai tuni ƙasar ta Sanarwa Limamai dasu Jagoranci Sallar Tarahiwihi, waɗanda suka haɗar da Shaikh Ab Badr Al Turki, Shaikh Al walid Al Shamsaan da kuma Shaikh Abdurrahman Sudais.
A ƙarshe Ƙasar Saudiyya ta yi fatan Allah yasa ayi Azumin dama sauran ibadun Allah karɓaɓɓu, kuma Allah ya hada Al’umma da dukkan Alkhairan dake cikin watan