An sace wani magidanci da iyalansa a Gusau, inda masu garkuwan suka nemi kudin fansa da sabon kudi.

0
79

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun yi garkuwa da mutane hudu da suka hada da namiji da mace da yara biyu a kauyen Kolo da ke karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.

An tattaro cewa bayan sace wadanda aka yi garkuwar da su, wadanda ake zargin sun bukaci a biya su N10m kuma sun ki amincewa da tsoffin takardun naira.

Wani dan asalin yankin mai suna Mohammed Ibrahim, ya ce daga baya ‘yan fashin sun rage kudin fansa zuwa N5m, inda ya ce mutanen kauyen sun yi ta kokarin tara kudin domin a sako wadanda lamarin ya shafa.

“A yayin da muke kokarin tattara kudaden da ‘yan ta’addan suka nema, sun sake aika da wani sako da safiyar yau cewa ba za su karbi tsoffin takardun naira ba.

“Sun ce za su ci gaba da ajiye wadanda aka sace a sansanonin su har sai an fitar da sabbin takardun Naira a watan Disamba,” in ji Ibrahim.

Kiraye-kirayen da aka yi wa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, da kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya ci tura.

Har yanzu ba a amsa sakonnin rubutu da aka aika zuwa lambobin wayarsu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

A wani labarin kuma a ranar Talata, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan siyasar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, Nduka Anyanwu, a jihar Imo.

An tattaro cewa, Anyanwu, wanda daya ne daga cikin ‘yan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar, yana yakin neman zabe tare da magoya bayansa, a lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye taron, suka sace shi.

Da take ba da labarin yadda aka yi garkuwa da shi, wata majiya ta ce, “’yan bindigar sun tare shi (Anyanwu) a hanya a lokacin da zai kammala shirye-shiryen gudanar da zaben wakilan sa. Har yanzu ba mu san inda suka kai shi ba kuma har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su yi wata magana ba.”

Da aka tuntubi shugaban jam’iyyar APGA a jihar, John Iwuala, wanda ya tabbatar da sace dan siyasar ya ce an sako dan siyasar.

Iwuala ya ce, “Eh, an yi garkuwa da dan takararmu da sanyin safiyar yau, amma a lokacin da muke shirin bayar da rahoto a hukumance, sai muka ji cewa masu garkuwa da mutane sun sako shi. Masu garkuwa da mutanen sun tattara duk abin da yake tare da shi kamar lokacin da aka yi garkuwa da shi.”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mike Abattam, ya ce har yanzu ba a sanar da shi lamarin ba.

 

Daga Fatima Abubakar.