Anci tarar Kano pillars Naira Miliyan 15

0
13

Anci tarar Kano pillars Naira Miliyan 15

Rawaitowa Daga Ghaddafi Isyaku Muhammad

 

An tuhumi ƙungiyar Kano Pillars da laifin karya dokoki da ƙa’idojin Nigeria Professional Football League, bayan wasan da ta buga a gida da Rivers United a ranar Lahadi, 19 ga Afrilu, 2026.

Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyar ta gaza samar da tsaro mai inganci a filin wasa, abin da ya bai wa wasu mutane damar kutsawa zuwa wuraren da aka hana shiga. Wannan lamari ya haifar da babbar barazana ga lafiyar ’yan wasa da kuma jami’an wasa.

Bugu da ƙari, wasu magoya bayan ƙungiyar sun shiga cikin filin wasa ba tare da izini ba, lamarin da ya saba wa ƙa’idojin gasar tare da jefa martabar wasan cikin haɗari.

Haka kuma, an zargi magoya bayan da aikata halaye marasa kyau da suka kai ga cin zarafi da tsoratar da jami’an wasa, abin da ya sa aka zubar da mutuncin gasar.

Hukunci da tarar kuɗi

Sakamakon waɗannan laifuffuka, an yanke wa Kano Pillars tarar kuɗi kamar haka:

Rashin samar da isasshen tsaro: Naira miliyan 4

Halayen rashin ɗa’a da suka bata sunan wasa: Naira miliyan 3

 

Rashin kula da halayen magoya baya (cin zarafi da tsoratarwa): Naira miliyan Munanan laifuka ga jami’an wasa: Naira miliyan 3

Haddasa tsaiko da katsewar wasa: Naira miliyan 2.Jimillar kuɗin da aka ci ƙungiyar ita Shi ne:Naira miliyan 15 (₦15,000,000)

Baya ga tara, an kuma hukunta Kano Pillars da buga wasanninta uku na gaba a gida ba tare da ’yan kallo ba.

Wasa ɗaya daga cikinsu zai kasance a wannan kakar, yayin da sauran biyun za su kasance a farkon kakar wasa mai zuwa.

Daga karshe An kuma bai wa ƙungiyar damar ɗaukaka ƙara cikin awanni 48 daga ranar da aka sanar da hukuncin.

 

Wallafawa Hafsat Ibrahim kawo