Rikideden Ido: Abubuwan Da Ya Kamata Iyaye Su Sani Game da Wannan Cutar

0
88

 

Idanun da suka rikide suna daya daga cikin matsalolin idanu da jarirai suka saba fuskanta.  Wannan cuta wacce kuma aka fi sani da strabismus yana  tafiya da kanshi, amma a wasu lokuta, yana kin tafiya.  A cewar Cibiyar Nazarin Ilimin Yara na Amirka (AAP), rikidewan idanu abu ne da ke iya faruwa da idanun jarirai tun daga haihuwa har izuwa kimanin watanni 4.  Dalilin haka shi ne, idanuwan jarirai ba sa iya mai da hankali sosai a watannin farko na rayuwa, wanda hakan ke sa idanuwansu  zagayawa ba tare da wani kamewa ba, wanda a wasu lokuta kan kai ga rikidewa ko fita waje ko ciki.  Duk da haka, idan hakan ya ci gaba bayan watanni 4, ya kamata ku tuntubi likitan jaririnku.

A cewar Cibiyar Kiwon Lafiya ta ƙasa, kusan kashi 4% na yara suna da idanu ɗaya ko duka biyun da ba daidai ba watto ya rikide.

Abin takaici shine, strabismus baya tafiya da kansa.  Hakanan yana iya haifar da asarar gani na dindindin idan ba a kula da shi ba.  Strabismus kuma na iya haifar da bibiyu ga yara.  Hakanan yana iya rinjayar gani, tare da ikon gani a cikin girma uku ko tare da asarar zurfin fahimta (stereopsis).  Iyaye ko jagora na iya gano wannan cuta a cikin ‘ya’yansu waɗanda har yanzu ba sa iya yin magana game da matsalolin gani ba, ta hanyar lura da yadda suke matse idonsu.  Yaran da ke fama da strabismus kuma suna iya juya ko karkatar da kawunansu don ganin abubuwa da kyau.

Idan ba a kula da strabismus ba, kwakwalwa za ta yi watsi da hoton da ido mai rauni ya samar, wanda zai haifar da amblyopia, ko “lazy eye.”  Amblyopia hasara ce ta dindindin da ba za a iya gyara ta da ruwan tabarau ko tabarau ba.  Amma idan an gano strabismus da wuri, ana iya magance shi ta hanyoyin nan:

  1. Rufe idanu

Rufe idon da ke da raunin zai ƙarfafa jijiyoyin idon na tsawon lokaci, tabbatar da cewa babu wani kaifin  Gani da ya ɓace da kuma maido da daidaituwar ido.  Ya danganta da tsananin matsalar, yara za su sa facin watto Rufe idon na tsawon sa’o’i 2-3 a kowace rana a cikin sa’o’in da idon su biyu na shekaru da yawa.  Ana iya Rufe idon na tsawon sa’o’i shida a kowace rana a wasu yanayi.

  1. Diga atropine.

Aikin atropine kamar Aikin Rufe idon ne.

  1. Gilashin

 

A wasu yanayi, sanya tabarau na iya taimakawa wajen daidaita idanuwa, tabbatar da cewa an samu alaƙa tsakanin kwakwalwa da idanu yadda ya kamata.

  1. Hanyoyin tiyata.

Wannan hanya ita ce abu na ƙarshe da za a yi amfani da shi idan tabarau, digon magani, da Rufe idon sun kasa daidaita idanu.

Idan kun ga wasu canje-canjen a idanu (ko rashin lafiya) a yaranku, kada ku jinkirta zuwa asibiti.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho