BABU RUFIN ASIRI GA DUK WANDA KE DA HANNU A FATAUCIN MIYAGUN KWAYOYI.NDLEA.

0
63

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA,ta sha alwashin cewa, ba wani rufa-rufa ga duk wanda ke da hannu ko alaka da fataucin miyagun kwayoyi,lamarin da ya shafi tsohon kwamandan leken asiri ta kasa IRT ta hukumar leken asiri ta Force Intelligence Bureau (FIB)na rundunar yan-sandan Nijeriya,Abba kyari.

Kakakin hukumar ta NDLEA Femi Babafemi,ya tabbatar da cewa, ba gudu ba ja da baya,domin hukumar a shirye take da ta tona asirin duk wani mai alaka da rikicin komai shekarun sa ko mukamin sa.

Femi ya kara da cewa, duk wanda ake tuhuma dole a gurfanar da shi gaban doka,don shine matsayin aikin shugaban mu,Brig.janar Muhammad Buba Marwa.

Don haka, muna kira ga yan Nijeriya, da su bar hukumomin da suka dace,su gudanar da binciken su yadda ya kamata,sannan da ga baya zamu bayyana muku sakamakon binciken mu.

An wallafa sunayen wayan da ake zargin kamar haka:

1-DCP ABBA KYARI

2-ACP SUNDAY J UBUA

3-BAWA

4-INSPECTOR SIMON AGIRGBA

5-INSPECTOR JOHN NUHU

BY FATIMA ABUBAKAR