Dimples ƙananan ramuka ne akan fata waɗanda ake iya gani a sassa daban-daban na jiki. Akwai nau’ikan iri biyu daban-daban, na wucin gadi da na dindindin. Ko da yake mafi yawansu suna kan kunci, ana iya gani sa a kusan ko’ina a jiki, a kafadu, a saman kugu har ma da baya. Sassan jiki da ya fi kowane samun dimples bayan kumatu shine haba. Yayin da wasu na iya korafin samun dimples a wasu sassan jikinsu, dimples da ke fitowa a kumatu da haba da kugu ana kallonsu a matsayin alamar kyau da kyan gani kuma suna da kara kyau.
A hakikanin gaskiya dimples, duk inda aka same su a cikin jiki, suna faruwa ne saboda nakasa a cikin tsoka ko haɗin tissue a wannan yanki. Ana ganin ramin dimple a mata da maza. Dalilin faruwar sa shine cewa akwai girma mara kyau a cikin tsoka a fuska yayin ci gaban embryonic . Yayin da tsokar fuska, wacce ke da alhakin daga leɓe sama yayin murmushi, ta kasu kashi biyu, ana samu ƙaramin rami tsakanin waɗannan sassa biyu, wadda fatar kumatu ke rufe shi. Saboda haka, duk da cewa ana daukarsa a matsayin nakasar kwayoyin halitta, idan mai dimple ya mike fuskarsa da tsokoki don yin dariya, ramuka masu ban sha’awa suna bayyana. Dimples akan kumatu suna faruwa ne saboda dalilai na kwayoyin halitta. Idan aka samu dimple a daya daga cikin iyayen, yuwuwar yaron ya samu dimple ya kai kashi 25-50%, yayin da yake tsakanin kashi 50-100% idan iyaye biyu suna da shi. A wasu lokuta ko da iyaye ba su da dimples a kuncinsu, akwai yiwuwar samunsa a cikin ‘ya’yansu.
Samuwar dimple na haba, wanda shine wani nau’in dimple da ake gani a wurin fuska, ba shi da alaƙa da tsokoki. Dimple na haba yana faruwa ne saboda rashin cikar hadewar rabi biyu na kashin muƙamuƙi. Wannan nakasar tana faruwa ne yayin ci gaban embryonic kamar yadda yake a cikin sauran. Kamar dimples na kumatu, fata ta rufe wannan tsari mai ban mamaki kuma haka ya haifar da wani rami mai kyau a ƙarƙashinsa. Ramin dimple wanda ba ya da wani mummunan tasiri a kan lafiyar ɗan adam ana maraba da shi kuma wani lokacin abin sha’awa a yawancin al’adu. Dimples, musamman wadanda ke kan fuska da kuma na saman kugu suna kara wa mutum kyau. Dimple, a matsayin ma’aunin kyau a duniya, yana ba da siffa mai kyau ga fuskoki yayin da take sassauta yanayin fuska. Ko a wasu al’ummomi an yi imanin dimple yana kawo sa’a kuma ana kiransa the angel touch . Ko da yake ana haifan mutane masu sa’a da wannan fa’idar adon, kuma yana yiwuwa a ƙirƙiri dimples ta hanyar tiyata ga masu son samun ɗaya.
Mafi yawan nau’ikan dimples da aka kirkira ta hanyoyin kwalliya sune dimples na kunci ko dimple na baya wanda kuma ake kira Venus dimple.
Wani nau’in dimple din da mutane ke ganin kyaun sa shine Venus dimple wanda ake kira back dimple pits. Wannan dimple da ke faruwa da kansa a jikin wasu mutane ramuka ne masu daidaituwa a ƙarƙashin yankin kugu, nesa da 6 zuwa 8 cm daga juna.
Firdausi Musa Dantsoho