Mawaki Davido ya nemi afuwar magoya bayansa, yayi alkawarin kawo wasansa na Timeless jihar Delta

0
40

Fittaccen Mawakin Afrobeats Davido ya rubuta sakon neman afuwa ga magoya bayan sa na jihar Delta wadanda suka ji takaicin rashin zuwansa taron Warri Again wanda aka gudanar a ranar 6 ga Oktoba, 2023.
Davido ya kasance a tsakiyar wata cece-kuce game da rashin ganin sa a taron Warri Again wanda Amaju Pinnick ya shirya.

A cewar tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick, wadanda suka shirya gasar sun biya Davido dala 98,000 inda suka kuma ware dala 18,000 kan wani jirgin sama mai zaman kansa da zai yi jigilar dan wasan zuwa jihar Delta.

Da yake jawabi a wajen taron, Pinnick ya ce Davido ya kasa zuwa duk da amincewa da ranar da kuma karbar kudin.
Davido ya mayar da martani ga Pinnick a jerin rubuce-rubucen da ya yi a kan X (Twitter) da kuma labarinsa na Instagram inda ya zargi tsohon shugaban NFF da kasancewar shi mai kula da kwallon kafa wadda ake cin hanci da rashawa a karkashin jagorancinsa wadda ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya ke bin albashi da alawus alawus.
Amaju Pinnick a cikin jawabinsa ya bayyana cewa ba za a sake maraba Davido ba a jihar Delta kuma a nasa martanin fitaccen mawakin ya bayyana cewa babu wanda zai iya hana shi yin wasa a kowane bangare na kasar Najeriya.

Da yake ba magoya bayansa hakuri a shafinsa na Instagram, Davido ya ce tuni ya sanar da masu shirya wasan na Warri Again game da gazawarsa ta halartar wasan saboda ya ci karo da rana daya da wani wasan sa da ya yi a New Zealand amma kuma masu shirya wasan sun ci gaba da inganta shirin ta hanyar amfani da sunansa.
Davido ya nemi afuwar magoya bayansa na Warri wadanda suka ji takaicin rashin zuwansa kuma ya yi alkawarin kawo wa jihar Delta wasansa mai suna “Timeless Xperience Concert” nan ba da jimawa ba.

Bayan fitowar albam dinsa na hudu ‘Timeless’, Davido ya shirya wasannin na Timeless a dandalin Tafawa Balewa Square Legas. Tare da alƙawarin da ya yi wa magoya bayansa na Jihohin Delta, cewa wasansa na biyu na Najeriya na iya kasancewa a jihar.

Firdausi Musa Dantsoho