CEO Tozali TV. Ta taya ‘yan kasar Nan Murnar Zagayowar Ranar Samun Ƴancin Kan

0
52

Mamallakiyar Gidan Jarida da Tashar Tozali, ta taya ‘Yan Najeriya murnar cika shekaru 65 a tafarkin Dimokuradiyya,.

 

Adan haka take qara tunasar da Al ummar kasar Nan Tarihin

Ranar Ɗaya ga watan Oktoba, wacce ta kasance Rana mai muhimmanci ga Najeriya. A ranar ce aka sauke tutar Ingila, aka ɗaga Fari da Kore, wato; Tutar Najeriya. A lokacin an yi murna da alfaharin samun Ƴancin Kai.

Matasa kamar su: Nnamdi Azikiwe, da Herbert Macauly, da Obafemi Awolowo, da Sir. Ahmadu Bello Sardauna, da Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa, da Aminu Kano, da Alh. Mudi Spikin, da Sa’adu Zungur, duk sune su taka rawar gani wajen ganin wannan Rana.

An fafata tsakani, kafin Turawan Mulkin mallaka suka bar Nahiyar Afirka. A wasu Ƙasashe sai da aka yi Yaƙin sunƙuru, wasu ma Turawa suka yi kaka-gida, in da suka mayar da ƴan asalin Ƙasar Bayi, marasa galihu, yayin da da ƙyar suka ƙwaci kansu!

An sadaukar da bauta don a samu ƴancin tafiyar da lamura, a lokacin an ƙawata Fadoji da Gidajen Gwamnati da Gadoji. An yi murna ganin irin burin da matasan suke da shi wajen jan ragamar jaririyar ƙasar ya cika.

Ana ganin nan gaba Najeriya za ta taka rawar gani a idon Duniya wadda ya haɗa da samun ci gaban Masana’antu da bunƙasar tattalin arziki.

A haka kowace shekara ake gudanar da shagulgula duk lokacin da ranar ta kewayo don tunawa da nasarar ranar.

Daga ƙarshe! Babu abin da ƙasar Najeriya ke buƙata da ya wuce addu’a daga bakunan Yara da manƴa, musamman domin lumana tsakanin ƙabilu da addinai,

 

Tozali TV Idonku ako ina.

 

 

Hafsat Ibrahim