Da Dumi-Dumin sa.Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jahar Anambra ya kwanta dama.

0
46

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Anambra, Nnamdi Okafor ya rasu.

Kafin rasuwarsa, Okafor, wanda aka fi sani da Akajiugo Awka, ya wakilci mazabar Awka ta Kudu 1 a majalisar dokokin jihar.

Har yanzu babu cikakken bayani game da mutuwarsa, sai dai wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce dan majalisar ya kwanta dama ya mutu da sanyin safiyar Laraba a wani otal da ke birnin Sandton na birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, kuma an tabbatar da mutuwarsa sa’o’i kadan bayan haka.

Marigayin da sauran ‘yan majalisar dokokin jihar sun tafi hutun majalisa.

Kawo yanzu dai ba a tantance cikakken bayanin musabbabin mutuwarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Cikakkun bayanai daga baya…