Dalilin Da Yasa Tambuwal Ya Sauka Wa Atiku inji Kakakin tambuwal

0
76

Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Tambuwal (TCO), Prince Daniel, ya bayyana dalilin da ya sa Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya ajiye mukaminsa ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da aka kammala a ranar Asabar da ta gabata.

Atiku ya lashe zaben ne da kuri’u 371 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, wanda ya samu kuri’u 237 bayan Tambuwal ya janye wa Atiku.

Kakakin ya ce Tambuwal ya sauka ne sakamakon kishin kasa da yake nuna wa ci gaban Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa; “Mai Girma Gwamnan Jihar Sakkwato Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, CFR na taya tsohon mataimakin shugaban kasa Alh. Atiku Abubakar, GCON a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben fidda gwanin da aka kammala.

“Gov. Tabuwal ya yanke shawarar janyewa daga takarar duk da cewa ya fi son ya ci tikitin ne saboda tsananin kaunar Najeriya da jam’iyyar musamman.

“Ga dimbin magoya bayanmu muna so ku sani cewa mun dauki wannan matakin ne dan kishin kasa, inda muka sanya kasarmu Najeriya da jam’iyyarmu ta PDP gaba da burinmu na kashin kai wanda muka sake nanata cewa bai kai muradin kasa ba.”

“Duk da haka, domin tabbatar da samun nasara a zaben yayin da PDP ke shirin kayar da APC a zabe mai zuwa na Fabrairu 2023, ya bukaci Wazirin Adamawa da su gudanar da yakin neman zabe wanda zai hada kan jam’iyyar da kasa baki daya.

“Mai martaba ya kuma yi matukar godiya ga shugaban kwamitin yakin neman zabensa bisa jagoranci nagari, da daukacin tawagar da dukkan wakilansa da kuma dumbin magoya bayansa a fadin kasar nan kan irin goyon bayan da suka bayar kafin taron da kuma bayan taron.

 

Daga: Firdausi Musa Dantsoho