Harin Jirgin Kasa: Kuna Iya Sauraron Waɗanda Akayi Garkuwa Da Ko kuma Ku Yi Watsi Da Su, In ji ɗan Ta’adda Ga Gwamnatin Taraiyya

0
105

 


Daya daga cikin ‘yan ta’addan da suka kama fasinjojin jirgin kasa da aka kai wa hari a Kaduna ranar 28 ga watan Maris, ya ce gwamnatin tarayya na da zabin sauraron wadanda abin ya shafa ko kuma ta yi watsi da su.

 

Dan ta’addan da ya rufe fuska ya yi magana a wani sabon faifan bidiyo inda takwas daga cikin wadanda abin ya shafa – mata uku da maza biyar – suka roki Gwamnatin Tarayya ta taimaka.

 

Mutumin da ya yi magana da turanci ya ce, “Mu ne mutanen da suka yi awon gaba da wadannan mutane daga jirgin Abuja zuwa Kaduna, don haka suna kira gare mu cewa suna son tattaunawa da gwamnatin tarayya, kuma mun ba su damar yin magana. Ya rage a gare ku ku saurare su ko ku yi watsi da su.”

 

Wata da aka kama, mai suna Mariam Abubakar, ta ce ‘ya’yanta sun yi rashin lafiya a hannunsu.

 

“Ina daya daga cikin wadanda aka kama a cikin jirgin tare da ’ya’yana hudu da mijina. Muna kira ga gwamnatin tarayya, iyalanmu da duk wanda zai iya don Allah a kawo mana agaji. Mun kasance a nan har tsawon kwanaki 62 kuma yanayin rayuwa mara kyau wanda ba a iya misaltawa.

 

“Mun yi rashin lafiya. Hasali ma, daya daga cikin ’ya’yana, biyu daga cikinsu ma ba su da lafiya a halin yanzu ba su da magunguna. Don haka muna rokonku da ku kawo mana agaji,” inji ta.

 

‘Yan uwan ​​wadanda abin ya shafa dai sun yi ta kiraye-kirayen a sake su, inda gwamnatin tarayya ta ba da tabbacin daukar matakin ceto fasinjojin.

 

Daga: Firdausi Musa Dantsoho