Yan sandan jahar Kano sun kama wani dan Kasar Sin da ya kashe budurwar sa da wuka.

0
159

Wani dan kasar China ya daba wa masoyiyar sa mai suna Ummakulsum Sani Buhari wuka har lahira a gidan Janbulo da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano a ranar Juma’a.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ‘dan kasar Sin ya ziyarci marigayiyar mai shekaru 23 a gidan iyayenta.

An ruwaito cewa marigayiyar wadda aka fi sani da ‘Ummita’ ta yi makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta Kano.

An tattaro cewa sun sami rashin fahimtar juna tsakanin su biyun ne ya haddasa lamarin.

“Ana  zargin ya kira Ummita akai-akai kuma an ce ta yi watsi da kiran nasa.

“Daga baya ya nufi gidansu Ummita inda yayi ta bugub k’ofar su ba kakkautawa hakan yasa mahaifiyar Ummita ta fusata.”

Da take magana,mahaifiyar marigayiyar ta bukaci a yi mata adalci yayin da take ba da labarin abin da ya faru tsakanin ‘yarta da dan China.

“A cewar ta ina son hukumomi su ga wannan aika aika. Sun dade da gama soyayyar su. Ta yi aure daga baya ta rabu da mijin ta. A lokacin ne ya dawo rayuwarta, yana matsawa dole ya gan ta.

“Ya kasance yana shigowa duk da ba mu son hakan amma bai gane ba. Mun kasance muna korar shi. Lokacin da na yi ƙoƙarin sanar da ’yan sanda, ’ya’yana  suka hana ni, su ka ce kada mu kai ga jama’a.

“Mutumin da ya zo taimakonta ya bi ta taga shi ne ya kama shi ya fito da shi.

“Ya gudu, suka kore shi, suka dawo da shi. Yanzu haka yana hannun ‘yan sanda. Ita ce babbar ’yata amma tana da ’yan’uwa maza biyu.”inji ta.

 Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

In da ya ce hukumar ta ‘yan sanda na ci gaba da bincike akan lamarin.

Daga Fatima Abubakar.