Davido da Chioma sun rasa dan su daya tilo Ifeanyi a jiya.

0
33

Labarin rasuwar dan  mawaki Davido ya watsu a kafafen sada zumunta daban-daban.Rasuwar dan farko a wurin Davido, Ifeanyi, ya sa wasu daga cikin masoyansa cikin alhini.

An ce Ifeanyi ya nutse ne a cikin ruwa na shakatawa da ke gidan mawakin da ke unguwar Banana Island a jihar Legas.

Yayin da wasu masu amfani da shafin Twitter ke nuna alhininsu, wasu kuma sun rataye ne da fatan cewa labarin karya ne.

Wata mai suna Peace Agina, ta bayyana raɗaɗinta tana mai cewa, “Rasuwar ɗan Davido da Chioma abin baƙin ciki ne.. Wannan abin bakin ciki ne kwarai. Ina rokon Allah Ya jikan su.”

Masu nishadantarwa da yawa sun yi ta’aziyya tare da Davido, Chioma bisa rasuwar dan su.

Wani ‘tabbacin’ kamar yadda Davido, Chioma su ka  sake farfado da soyayya a kwana kwanan nan.

Wani tweep, Mista Walter ya ce, “Mutuwar yaron ya kasance abin ban mamaki,  Ta’aziyyata ga Davido, da masoyiyarsa, Chioma. Allah ya basu ikon jurewa wannan rashi. Wannan abin bakin ciki ya sa masana’antar nishaɗi ta duniya ta ji rauni.”

Wani tweep, Mista Sam, ya bayyana imaninsa cewa Ifeanyi yana raye kuma ya ce, “Har sai Davido ya yi rubutu game da hakan, Ifeanyichukwu na raye,inda ya ke fatan kar Allah ya sa ýa ga mutuwar ‘ya’yan sa, Amin.”

Oluwadamilola90,shima  ya yi fatan samun amsa mai kyau daga Davido yana mai cewa, “Muna jiran labarai masu inganci daga #davido tun daren jiya. Inda ya ce Allah Ya ba su dangana..”

Daga Fatima Abubakar.