Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura sunan Murtala Garo domin mataimakin gwamna a Kano
Daga wakilin mu Ghaddafi Isyaku Muhammad
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunan Hon. Murtala Sule Garo ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantance shi a matsayin mataimakin gwamna.
Sanarwar hakan ta fito ne ta hannun mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya bayyana cewa an riga an aika da sunan domin fara tantancewa kamar yadda doka ta tanada.
Wannan mataki na zuwa ne a wani lokaci da siyasar jihar ke ɗaukar sabon salo, musamman wajen cike gurbin muƙamin mataimakin gwamna.
Majiyoyi sun ce ana sa ran Majalisar Dokokin Jihar Kano za ta fara duba cancantar dan takarar nan ba da jimawa ba, inda za a tantance kwarewarsa, gogewarsa da kuma dacewarsa da wannan muƙami mai muhimmanci.
Sai masu sharshi na Ganin wannan mataki na gwamna na iya haifar da muhawara a tsakanin al’umma da ‘yan siyasa, musamman duba da rawar da muƙamin mataimakin gwamna ke takawa a tafiyar da harkokin mulki a jihar.
Har yanzu dai ana jiran karin bayani kan matakan da za su biyo baya daga bangaren majalisa, yayin da jama’a ke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan wannan sabon nadi na Mataimakin gwamnan.
Wallafawa Hafsat Ibrahim


