Hadaddiyar Daular Larabawa Ta Bayyana Makokin Kwanaki 40 Yayin Da Shugaban Kasa Ya Mutu

0
203

Kamfanin dillancin labarai na kasar WAM ya ruwaito haka a safiyar Juma’a.”Ma’aikatar Harkokin Shugaban Kasa ta yi ta’aziyya ga mutanen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma duniyar Musulunci… a kan rasuwar Sheikh Khalifa bin Zayed Al-Nahyan a ranar Juma’a, 13 ga Mayu,” a cewar kamfanin dillancin labarai na kasar,Da yake tsokaci kan wannan mummunan labari, Yarima mai jiran gado na Abu Dhabi, Mohamed bin Zayed Al Nahyan, ya ce Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi rashin da da shugaba adali.

Ma’aikatar ta ba da sanarwar kwanaki 40 na zaman makoki tare da rage tutoci zuwa kasa  daga ranar Juma’a, tare da dakatar da ayyukan gwamnati da masu zaman kansu na kwanaki uku na farko.

Sheikh Khalifa ya zama shugaban UAE na biyu a watan Nuwamba 2004.Ya gaji mahaifinsa a matsayin sarkin Abu Dhabi na 16.A karkashin kundin tsarin mulkin, mataimakin shugaban kasa kuma firaministan kasar Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum, mai mulkin Dubai, zai yi aiki a matsayin shugaban kasa har sai majalisar tarayya wadda ta hada da sarakunan masarautun bakwai za su hadu a cikin kwanaki 30 don zaben sabon shugaban kasa.Khalifa, wanda aka haife shi a 1948, ba a cika ganin shi a bainar jama’a ba tun bayan fama da bugun zuciya a shekarar 2014. 

ALLAH YA JIKANSA DA RAHAMA, AMEEN.

 UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.