Halaka kwabo alawa ne da akafi sanin shi a arewacin kasar nijeriya, ana yin shi ne da soyyayen gyada da narkaken siga sa’anan a sanya masa wasu sinadaran kamshi din kara masa dandano.
Halaka kwabo na da saukin haddawa ga kuma daddi. Wannan alawan na daukan minti goma wajan haddawa.
ABUBUWAN BUKATA SUNE:
- Gyada kofi biyu
- Siga kofi daya
- Vanilla flavor karamin cokali daya
- Citta rabin karamin cokali
- Kanumfari rabin karamin cokali
- Man zaitun ko kuma man gyada
YADDA AKAE HADAWA
- Da farko zamu dan barza gyadan mu, yadda zai farfasu kanana.
- A cikin tukunyan suyan mu, zamu zuba sigan mu muyi ta juyawa har sai ya narke ya chanja kala zuwa brown.
- Sai mu zuba vanilla flavor inmu a ciki mu kashe wutan sai mu juya shi sosai ya hadu.
- Sai mu zuba garin citta da kanunfari a ciki, mu zuba barjejen gyadan mu a ciki sai mu kunna wutan muyi ta juya.
- Muna juyawa zamu gan ya hade sai mu dauko man zaitun mu zuba a ciki muna zubawa sai mu kasha wutan kuma.
- Bayan mun kashe wutan kar mu daina juyawa, mu cigaba da juyawa.
- Sai mu kara kunna wutan mu amma mu rage wutan sosai ma’anna wutan ya kasance on a very low heat.
- Sai mu juye haddin mu a tray mu baza zai mu yanyanka mu barshi yayyi karfi.
- Toh halaka kwabon mu ya haddu.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho