Hanya mafi sauƙi don hadda Nkwobi mai daɗi

0
316

 

 

Yawanci, ana amfani da kanwa don haɗa shi, amma za ku iya maye gurbinsa  da abun da aka fi sani da ncha ko ngo wanda ya fi kyau ga  lafiya, ba ya kumbura ciki  kuma ba zai sa ku yi zawo ba.

Abubuwan bukata sune:

*Kafar saniya

*Man ja

* Kanwa

*NikakkenKa kwallon ehuru 

*Crayfish nikakke

* Barkono nikakke

* Attarugu 

* Albasa

* Kayan dandano

* Gishiri 

* Ganyen Utazi 

Yadda Ake hadda Nkwobi Kafar saniya

  1. Da farko zaki yanka ƙafar saniya zuwa girman da kike so, sai ki wanke, ki sa a cikin tukunya.
  2. Sai ki sa sinadaran dandanon ki, kayan kamshi, yankakken albasa da ruwa kadan sai ki rage wutan zuwa matsakaicin zafi har sai ya dahu sosai. Sai ki sa gishiri, ki motsa kuma ki tabbatar da cewa babu wani sauran ruwa a ciki.
  3. A cikin wani kwano, sai ki hada kanwan ki da ruwa kadan sai ki motsa. Sai ki tace hadin da kyau a cikin wanni kwano mai kyau  sannan ki ajiye a gefe.
  4. Ki zuba man jan ki  daidai a cikin busasshiyar tukunyar ki da aka bushar sannan a zuba hadin da aka tace a ciki kadan_kadan, ana rika motsawa da muciya har sai man jan ya koma rawaya kuma ya yi kauri.
  5. Sai ki sa crayfish nikakke, barkono da  ehuru. Sai a juya sosai har sai komai ya haɗu yada ya kamata 
  6. Sai a zuba  ƙafar saniya da aka dafa a cikin man jan kuma a motsa sosai tare da muciya.
  7. Sai a mayar kan murhu a dumama.
  8. Toh Nkwobi ya hadu sai a  shirya nkwobi a kwano A yi masa ado da zoben albasa da yankakken ganyen utazi.

By: Firdausi Musa Dantsoho