Hanyoyi uku da zamubi wajen gyaran fuskar mu

0
71

Fuskar mu tana da matukar amfani a garemu yaka mata a kullun gyara shi. Ga hanyoyi uku da zaki bi don gyara fuskan ki yayi laushi, kyau da sheki.
1. Ki samu cucumber sai ki yayyanka kisa a blender ki nika ya niku, sai ki samu ruwan rose da lemon tsami ki hada su a waje guda, sai ki shafa a fuskan ki da daddare ki bari gari ya waye sannan ki wanke, hakan zai baki fuska mai laushi da sheki.
2. Ki samu karas ki yayyanka ki markada sai ki shafa a fuskan ki, ki bari yayi awa biyu sannan ki wanke da ruwan dumi, zakiga fuskar ki ta kara haske da sheki.
3. Ki samu lemon tsami ki yanka shi gida biyu ki dauki Rabin kisa Zuma akai, sannan ki goge fuskar ki dashi musamman inda yake da kuraje da tabo ki bari yayi minti biyar sai ki wanke da ruwa. Zakiga fuskar ki tayi tsantsi, laushi da sheki.
rinka

Daga faiza A.gabdo