HUKUMAR BABBAN BIRNIN TARAYYA (FCTA)TA DAUKI KARIN MATAKAI DON KARFAFA TSARIN RIGAKAFIN YAU DA KULLUM.

0
90

Hukumar babban birnin tarayya Abuja ta dauki karin matakai don karfafa dukkanin tsarin rigakafi na yau da kullum a fadin hukumomin shida na yankin.

Karamar ministan babban birnin Dokta Ramatu Tijjani Aliyu ta bayyana cewa gwamnati zata yi bakin kokarinta don ganin tsarin kawo lafiya a matakin farko a birnin,domin shine burin shugaba Muhammadu Buhari.

Ministan ta shaida hakan ne a taron farko na komitin FCT kan shirin kawar da cutar polio da kuma rigakafi na yau da kullum ta shekara 2022 don tattaunawa da tsara dabarun ayyukan rigakafin.

Aliyu Wanda babban mataimaki ne na musanman kan harkokin milki ,Wanda ferfesa Muhammad Usman Ya wakilta,ya bayyana cewa,ta hanyar asusun samar da kiwon lafiya na asali,tuni hukumar ta fara gyara kayan aikin kiwon lafiya a mataki na gaba da shigar da karin ma’aikatan lafiya,da samar da magunguna masu inganci don kara karfafa ayyukan kiwon lafiya .

A nasa jawabin sakataren ma’aikatan lafiya da jin dadin al’umma Dokta Abubakar Tafida Ya bayyana cewa sakateriyar zata tura tawagara mutum 1,639 a cikin kwanaki hudu da za su fara daga ranar 22 ga watan junairun domin yiwa yara ‘yan kasa  da shekaru biyar cikin al’ummomi 2837 a fadin  yankin.

By fatima Abubakar