Fa’idodin 8 da Azumin keyi ga Lafiyar Jama’a.

0
145

Duk da karuwar shaharar da ya yi a baya-bayan nan, azumi al’ada ce da ta samo asali tun shekaru aru-aru kuma tana taka rawa a cikin al’adu da addinai da yawa.

An ayyana shi a matsayin kamewa daga duk wani abinci ko abin sha na wani ƙayyadadden lokaci, akwai hanyoyi da yawa na azumi.

Gabaɗaya, yawancin nau’ikan azumi ana yin su ne sama da sa’o’i 24-72.

A daya bangaren kuma, azumi na zagawa ne tsakanin wasu lokutan cin abinci da azumi, daga sa’o’i kadan har zuwa wasu kwanaki a lokaci guda.

An nuna cewa azumi yana da fa’idodi da yawa na kiwon lafiya, tun daga yawan rage nauyi zuwa ingantaccen aikin kwakwalwa.

Anan na kawo muku fa’idodin azumi ga kiwon lafiya guda 8 – wanda kimiyya ta amince dashi.

  1. Yana da amfani wajen taya rage Ciwon sukari na jini ta hanyar Rage Insulin.

Yawancin bincike sun gano cewa yin azumi na iya inganta sarrafa sukari a cikin jini, wanda zai iya zama da amfani musamman ga masu fama da ciwon sukari. A gaskiya ma, binciken daya a cikin mutane 10 masu fama da ciwon sukari  ya nuna cewa azumi na ɗan gajeren lokaci yana rage yawan matakan sukari na jini.

  1. Yana Samar da Ingantacciyar Lafiya ta hanyar Yaki da Kumburi

Yayin da kumburi mai tsanani shine tsarin rigakafi da ake amfani dashi don taimakawa wajen yaki da cututtuka, kumburi na kullum zai iya haifar da mummunan sakamako ga lafiyar ku. Bincike ya nuna cewa kumburi na iya faruwa cikin ci gaban yanayi na yau da kullun, kamar cututtukan zuciya, ciwon daji da cututtukan fata (4), don hakane yasa Wasu nazarin suka gano cewa azumi zai iya taimakawa wajen rage yawan kumburi da kuma taimakawa wajen inganta lafiya.

  1. Azumi na Iya kara Ƙarfafa Ayyukan Ƙwaƙwalwar Dan Adam.

Bincike da yawa sun gano cewa azumi na iya yin tasiri mai karfi kan lafiyar kwakwalwa. Ɗaya daga cikin binciken da akayi ya nuna cewa yin azumi na tsawon watanni 11 ya na inganta aikin kwakwalwa da tsarin kwakwalwa .

  1. Yin Azumi Yana Taimakawa Wajen Rage Nauyi

A ka’ida, kaurace wa duk ko wasu abinci da abubuwan sha  suna taimakawa wajen rage yawan adadin calorin na mu, wanda zai iya haifar da rage nauyi ga jikinmu.

Wani bincike ya gano cewa azumi na tsaka-tsaki a kan makonni 3-12 ya kasance mai tasiri wajen haifar da asarar nauyi matuka.

  1. Azumu na Taimakawa Kan Rigakafin Ciwon Sankara.

A cewar masu nazari da gwajin-tubu sun nuna cewa azumi na iya amfani da magani wajen rigakafin ciwon daji.

ummu khulthum Abdulkadir.