Jaruman Kannywood mata Da Suka janyo cece ku ce a shafukan Sada zumunta

0
231

 

 A yayin da jaruman Kannywood ke ci gaba da fuskantar kalubalen sana’a da zamantakewar al’umma a muhallinsu, wasu ‘yan wasan kwaikwayo mata sun tsunduma cikin  cece-kuce a tsawon shekaru nan.

 

Daga cikin irin wadannan al’amura na baya-bayan nan har da cece-kucen da ya biyo bayan wata magana da fitacciyar jaruma Nafisa Abdullahi ta yi game da iyaye su daina haihuwan yayan da bazasu iya kula dasu ba. Baya ga Nafisat Abdullahi , Akwai wasu ’yan fim guda hudu na Kannywood da suka janyo cece kuce a shafukan yanar gizo .

Nafisat Abdullahi     

A ranar 16 ga Afrilu, nafisat ta wallafa a shafinta na Tuwita, “Ku daina haihuwa yayan da bazaku iya kula da su ba .”

Wallafar Tweeta din ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta, daga wasu ‘yan arewacin Najeriya da suka fassara shi da cewa kira ne da ya sabawa tsarin ilimin Alkur’ani da aka fi sani da “Almajiranci”, yayin da wasu ke ganin ba ta da ‘yancin da za ta magance matsalar zamantakewar al’umma. kasancewarta yar wasan kwaikwayo.

Nafisa ta dage cewa matsalar ba ta shafi ta ko wasu masu gata ba amma ga yara masu tasowa da iyayensu ke turasu zuwa tituna da sunan karatun Alkur’ani.

Rahma Sadau

Za’a iya kwatanta Rahama Sadau a matsayin jarumar da ta fi kowa janyo cece-ku-ce, a Kannywood wadda ta ke tattare da labaran cece kuce biyo bayan sana’arta a matsayin jaruma.

A shekarar 2016, an dakatar da ita daga yin wasan kwaikwayo a Kannywood saboda fitowar ta a wani faifan bidiyo na waka inda aka gan ta tana rungume da mawakin Najeriya, Classiq. Daga karshe dai an yafe mata sannan ta koma wasan kwaikwayo.

Jarumar ‘yar asalin jihar Kaduna da ke fitowa a fina-finan Kannywood da na Nollywood, ta kuma haifar da zazzafar cece-kuce a shafukan sada zumunta kan wasu hotuna da ta wallafa a shafukanta na Instagram da Twitter a shekarar 2020. Hotunan dai sun janyo cece kuce Inda har ya janyo batanci Ga manzon Allah hakan ya kasance cin mutunci ga musulman arewacin Najeriya. al’amarin da ya sa daga baya ta nemi gafara ta cire hotunan.

Sadiya Haruna

Sadiya Haruna wata jarumar fina-finan Kannywood ce da ta yi ta janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta kan yadda ta wallafa hotunanta da bidiyon tsiraicin da yawancin masoyanta ke ganin ba su dace ba.

A watan Fabrairu ne wata kotun majistare ta Kano ta yanke wa jarumar hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida ba tare da zabin tara ba saboda bata sunan wani abokin aikinsu, jarumi Isa A. Isa.

 Ana tuhumar jarumar da bata sunan Isa a wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta.

Fati slow

Jarumar Kannywood, Fati Usman, wacce aka fi sani da Fati Slow a kwanakin baya ta kasance abin ban dariya da cece-kuce a shafukan sada zumunta tsakanin ‘yan arewacin Najeriya.

A cikin watan Fabrairu ne ta shiga takaddama da fitaccen mawakin Hausa, Naziru Sarkin Waka, kan wani faifan bidiyo na TikTok da ta yi tana kiransa da mazinaci (a matsayin martani ga ikirari da mawakin ya yi na cewa wasu ’yan fim na neman yin lalata da ’yan fim mata kafin a raba musu matsayi a fim). Daga baya da ya bata kyautan naira miliyan 1 ta ce ta yi nadamar wannan zargi kuma ta nemi gafararsa.

Hadiza Gabon

Anyi cece kuce a shafukan sada zumunta yayin da a shekarar 2019 aka ga fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Hadiza Gabon, tana cin zarafin wata jaruma Amina Amal a wani hoton bidiyo na Instagram.

Gabon dai ta yi ikirarin cewa Amal na zarginta da kasancewa ‘yar madigo wanda hakan ya sa ta fusata ta dauki wani faifan bidiyo tana dukan Amal, lamarin da ya tilasta mata ta amsa zargin karya ne.

Bidiyon ya harzukar da mutani dama daga cikin mabiyan jaruman biyu, lamarin da ya sa wasu kungiyoyi suka yi barazanar kai karar Gabon saboda cin zarafi. An dai ce wasu masu ruwa da tsaki a harkar masana’antar ne suka sasanta ‘yan fim din biyu

Daga: Firdausi Musa Dabtsoho