Jarumi Ali Nuhu Ya wallafa Sabon Hoton Dan Sa, Ahmad A Yayin Da Yake Shirin Wasan Kwallon Kafa A Kasar Ingila

0
303

Iyaye da yawa suna ba wa ‘ya’yansu daman zabi a lokacin zabar abun da suke so su zama. Shahararren jarumin Kannywood Ali Nuhu ya baiwa dansa Ahmad abinda yake so, wato ya zama dan kwallon kafa.

Jarumin fina-finan Kannywood, Ali Nuhu ya samu karbuwa a lokacin da ya wallafa hotunan dansa , Ahmed, wanda zai buga wasan kwallon kafa a kasar Ingila. Ya yiwa Ahmed wasu kalamai na kwarin gwiwa yayin da yake shirin ranar wasa.
Ali Nuhu yana alfahari da dansa Ahmad domin yana taka rawar gani a fagen kwallon kafa a Ingila. Ga kayattattun hotona da bidiyon Ali Nuhu da dansa a ingila.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho