Jaruma rahma sadau ta wallafa hotonta da kakarta Yayyin da ta ziyarci kauyen su a jihar Gombe

0
157

Duk inda mutum ya je a rayuwa ba zai taba mantawa da gidansa ba. Shahararriyar Jarumar Najeriya, Rahama Sadau wacce aka fi sani da Jarumar Hausa a kwanakin baya ta watsa wasu Hotunan da ta ziyarci kauyen su a shafukan sada zumunta. Shahararriyar Jarumar, Rahama Sadau ta sanya hotonta dama bidiyo tare da kakarta a kauyen su da ta ziyarta a jihar Gombe.

An san Rahama Sadau a matsayin babbar Jarumar kasar Najeriya, mai shirya fina-finai, kuma mawakiya. An haife ta kuma ta tashi a jihar Kaduna, ta yi wasan raye-raye tun tana yarinya da kuma lokacin da take makaranta. Ta yi suna a karshen shekarar 2013 bayan ta shiga Kannywood.

Hakika Rahama Sadau tana alfahari da wannan sana’ar tata domin a yanzu tana fitowa a masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood a kasar Indiya.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho