Ko da ba zan iya biya tallafin yara ba, har yanzu tana bayyana ni a matsayin babban jarumi ga ɗanmu’ – Teebillz ya yaba wa Mawaƙiya Tiwa Savage

0
15

Tunji ‘Teebillz’ Balogun, tsohon mijin mawakiya Tiwa Savage, ya yaba mata kan sanya shi a matsayin jarumin uba ga dan su Jamal dan shekara takwas.

A cewarsa, ko da ba zai iya bada tallafin yaro ba, Tiwa har yanzu tana gabatar da shi a matsayin “superman” ga Jamal.

Shugaban mawakan ya kara da cewa yana daya daga cikin mazajen da suka yi sa’a wadanda suke da matsayin a wajen tsohuwar matar su saboda sauran mazan da yake gani a cikin yanayi guda suna shiga cikin hali mara daɗi.”

Ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Instagram a ranar Asabar.
Teebillz ya rubuta, “Lokacin da na ga abin da wasu maza ke ciki! Ba zan iya taimakawa ba sai dai in ƙidaya albarkata! Har abada ina godiya ga Mama J don sanya dangantaka ta ta kasance mai laushi da cike da ƙauna…..!

“Ko da ba zan iya biyan wasu kudi ba….. Har yanzu tana gabatar da ni a matsayin super man ga tagwaye na, kasancewar mahaifiya da bata da miji aikin ne babba…..! Godiya da Albarka Titi…H
Na godiya matuka.”

Teebillz da Tiwa Savage sun yi aure a watan Nuwamba 2013.

Ma’auratan sun yi maraba da dansu Jamal a shekarar 2015 kafin auren ya rabu a shekarar 2018 bayan zargin rashin haihuwa da kuma shan miyagun kwayoyi da su biyun suke zargin juna.

Firdausi Musa Dantsoho