Tsohon dan wasan Ingila, Heskey ya bukaci Liverpool da ta sayi Osimhen

0
18

Tsohon dan wasan Ingila Emile Heskey ya shawarci Liverpool da ta sayi Victor Osimhen.
Rahotanni sun bayyana cewa Liverpool na cikin kungiyoyin da ke son siyan Osimhen daga kulob din Napoli na Seria A.

Kungiyoyin Premier League, Chelsea, Tottenham Hotspur da Manchester United, da kuma zakarun Turai, Real Madrid ma suna zawarcin dan wasan na Najeriya.
Dan wasan mai shekaru 23 ya zura kwallaye 10 kuma ya taimaka aka zura kwallaye uku a wasanni 14 da ya buga a Napoli a bana.

Kwanan nan ne aka bai wa dan wasan Najeriyar lambar yabo a matsayin gwarzon matashin dan wasa na shekara a gasar kwallon kafa ta duniya a Doha, Qatar.

“Hakika (Osimhen) zai ba su wani abu daban da abin da suke da shi yanzu,” in ji Heskey. “Ya bambanta da Nunez wanda zai iya taka leda; Osimhen zai zama barazana ta tsakiya,” Heskey ya fada wa Anfield Watch.
“Yana da sauri, yana da ido don zura kwallaye, kuma yana iya gamawa sosai da ƙafafu biyu. Shi babban dan wasa ne. Ina tsammanin Napoli ta biya masa kuɗi da yawa, don haka ne za’ayi musayar sa akan fam €100m.

Osimhen ya koma Napoli daga kungiyar Ligue 1, Lille, a shekarar 2020 kuma yana da kwantiragi har zuwa 2025.

Napoli ba ta son sayar da Osimhen a watan Janairu, kuma za a yi duk wata yarjejeniya da za a yi a bazara mai zuwa.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho