Kotin Koli Ta Tabbatar Da Zaben Gwamnan Legas.

0
12

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Kawo Ƙarshen Shari’ar Sanwo-Olu Da Rhodes-Vivour

Kotun kolin kasar ta fara yanke hukunci kan rigingimun gwamnonin da suka taso daga zaben 2023.

Wani kwamitin alkalai bakwai na sauraron kararrakin zabe kan kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar Legas.

Kotun Kolin Nigeria ta tabbatar da zaben gwamna Babajide Sanwo Olu na jihar Lagas a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Kotun ta tabbatar da zaben nasa ne inda ta Kori karar dan takarar Gwamnan jihar karkashin tutar Jam’iyar LP, kamar yadda muka rawaito

 

Hafsat Ibrahim