Kungiyar JUAC ta garkame kofofin shiga FCTA da FCDA .

0
12

Yayin da yajin aikin gama gari da kungiyar kwadago ta kira ya shiga rana ta biyu, kungiyar FCTA/FCDA Labour, da hadin gwiwar kungiyar Action Committee, JUAC suka shiga aiki tare da rufe babbar kofar shiga harabar hukumar FCT.

Ma’aikata sun yi cincirindo a ƙofar yayin da shugabannin Labour suka tilasta su bin dokar “babu shiga, ba fita.”
Da yake magana da shugaban JUAC, Kwamared Mutilukoro Korede, ya ce za a ci gaba da daukar matakin har sai an biya musu bukatunsu.
Matilukuro ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya rage tafiyar sa ya dawo Najeriya ya yi abin da ya kamata.

Babban abin da suke bukata shi ne gwamnati ta yi Allah-wadai da zaluncin da aka yi wa shugabansu, shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero a jihar IMO da kuma wadanda suka aikata laifin a gurfanar da su.

Korede ya ce an cire tallafin man fetur wanda
hakan ya haifar da zafi kuma dole ne Shugaba Tinubu ya dawo ya sake dabara.

Kalamansa: “Har yanzu muna rera waƙa iri ɗaya, don biyan bukatar Labours.
“Ya kamata a yi Allah wadai da zaluncin Shugaban NLC gaba daya kuma a kama masu laifin tare da gurfanar da su gaban kuliya, musamman jami’an ‘yan sanda da abin ya shafa da sauran mutane.”

A cewarsa, dalili na biyu na yajin aikin shi ne irin wahalhalun da aka samu na cire tallafin man fetur da ya kamata gwamnati ta sake yin dabara.
“Wahalhalun da ake fama da su a kasar sun zama abin da ba za a iya jurewa ba, ba a bukatar karin farashin man fetur. Yanzu haka ‘yan Najeriya na cikin zafi. Suna biyan wani Naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi kuma zai a.kashe tsakanin N60,000 zuwa N70,000 na sufuri daga inda ake zaune zuwa ofis, ta yaya mutum zai  tsira?

Korede ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake yin dabara. “Suna bukatar su kalle shi ta wani bangare.
“Mun yi imani da Najeriya, mun yi imani da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. A nan FCT, mun yi imani da namu minista amma ba za mu yi shiru ba, a nan za mu tabbatar da cewa ƙofar ta kasance a kulle da maɓalli. Na san sauran abokan aikinmu a fadin kasar nan suma hakan  suka yi. Ba za mu tsaya ba har sai gwamnatin tarayya ta ga dalilin da zai sa ta yi wani abu.

“Shugaban ba ya kasar nan, idan muna da muhimmanci a gare shi ya rage tafiyarsa ya dawo gida, yana can ne saboda ‘yan Najeriya sun zabe shi ya zama shugaban kasa; gidan ku ba zai iya cin wuta ba kuma kuna jin daɗi a wani wuri. Ya kamata shugaban kasa ya dawo ya biya mana ukataun mu, kada ya sa mu yi nadamar zaben shi.

 

Daga Fatima Abubakar.