Kungiyar malamai ta kasa ASUU,ta tafi yajin aiki na wata daya,domin jan kunna ga Gwamnati.

0
22

ayan tattaunawa mai tsanani tsakanin membobin ASUU ta kasa baki daya,kungiyar malaman ta yanke shawarar tafiya yajin aiki na wata guda daga yau litinin 13 ga watan faburairun 2022,domin Jan kunne ga Gwamnatin tarayya,don ta gaggauta biya musu bukatun su.
A wata majiya a wurin taron da aka gudanar a jihar Legas, kungiyar ta ce muna son mu bai wa Gwamnati doguwar igiya da fatan za ta kaucewa gurgunta ayyukan ilmi a jam’iyoyin kasar nan.
A cewar su,muma iyaye ne,kuma muna da ‘ya’yan mu a cikin tsarin,amma ba za mu iya sa ido muna ganin tabarbarewar ilmi a kasar nan.
Majiyar ta kara da cewa,tashin hankalin mu yana da anfani ga kowa da kowa,kuma idan tsarin ya inganta ,duk za mu ji dadin sa.
Wasu fitattaun mutane a kasar sun shiga cikin lamarin ,amma bisa dukkan alamu Gwamnati ta ki ta saurara, don haka shugaban mu na kasa zai ba manema labarai karin haske daga baya.

By Fatima Abubakar