KUNUN MADARA (MILK PAP OR MILK PUDDING)

0
128

 

Kunun madara, kunu ne da keda daddi sha, ga kuma saukin yi, baya bukatan kashe kudade da yawa wajan hada shi, kuma madara shine abu mafi muhimmanci wajan hada shi.

ABUBUWAN BUKATA WAJAN HADA SHI SUNE:

 • Madaran gari kofi biyu
 • Siga yadda kake son yayyi zaki
 • Kuskus kofi daya
 • Kanunfari kwaya shida
 • Corn flour four babban cokali daya
 • Vanilla flavor
 • Dan kishiri kadan

 

YADDA AKE HADAWA

 1. Da farko zamu zuba ruwa kofi hudu a tukunya.
 2. Sai mu sa madaran mu kofi biyu a cikin ruwan mu gauraya ya hadu mu tabbatar babu guda gudan madaran.         
 3. Sai mu zuba gishiri kadan da kanunfarin mu, mu rufe tukunyanmu a barshi ya tafasu.
 4. Bayan ya tafaso zamu ji madaran mu na kamshi, sai mu saka kuskus in mu muyi ta gauraywa har sai kuskus in mu ya dahu.         
 5. Idan kuskus in mu ya dahu, mu zuba sikarin mu, sai mu dama corn flour in mu da ruwa yayyi kauri sai mu zuba a cikin ruwan madaran.
 6. Toh kunun madaran mu ya hadu asha lafiya.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here