MUHIMMANCIN ALLURAN RIGAKAFI GA YARA KANANA

0
513

 

Alluran rigakafi sunada matukar muhimmanci ga rayuwar yara kanana domin kuwa a wannan lokacin basuda wata wadatar wani garkuwar jiki da zai kare su daga kamuwa da cututtuka musamman daga ranar haihuwa har zuwa shekara biyar a rayuwa. Alluran rigakafin yara sun kasu kashi iri-iri wadda a kowane wata ana yinsa kama daga ranar haihuwa har zuwa lokacin da yaro zai shekara hudu zuwa biyar a duniya, wadannan allurai sun hada da  BCG,BPT,HPV,CSM, YELLOW FEVER DA KUMA MEASLES.Da sauransu.

Wadannan allurai suna kare yara daga kamuwa da cututtuka masu saurin hallaka yara kamar su tarin fuka,tarin shika ciwon shawara, ciwon hanta da dai sauran cututtuka masu matukar hadari ga lafiyarmu, haka zalika wannan allura ta rigakafin yara ba duka ne ake allura ba akwai wadda ana disawa ne abaki kaman su cutar shan inna,polio,sankarau da sauransu.ana fara wannan allura ne Jim kadan bayan an haifi yaro an tsabtaceshi a asibiti kuma shiyasa ake so ana haihuwa a asibiti domin yanada matukar amfani da zaran an haifi yaro kan ya koma gida ake mishi alluran farko na tarin fuka wato BCG.

Don haka iyaye mu kula sosai domin yiwa yayanmu wannan alura don kare su daga shiga cututtuka masu hadari, haka zalika ita wannan allura ba wai a lokaci daya ake yinsu duka ba tsakanin na farko da na biyu yana iya kaiwa kwana 40 wato mako 4 zuwa 6 amma ya danganta da bayanin maaikatan kiwon lafiya.

Haka zalika duk yaran da iyayensu ke kaisu asibiti don karbar alluran rigakafi ana ganinsu cikin koshin lafiya da kumari, ga kuma kaifin basira da girma cikin sauri, don haka iyaye mu kiyaye sosai wajen kai yayanmu gurin rigakafi domin inganta lafiyarsu muma kuma zamu samu kwanciyan hankali wajen rage kashe kudi zuwa asibiti.

 

BY:UMMU KHULTHUM ABDULKADIR