Majalisar wakilai ta ƙi yarda a yafe wa ɗalibai kuɗin WAEC da NECO da UTME da JAMB da su rubuta kyauta

0
22
A ranar Laraba 26 ga watan Oktobar 2023  ne Majalisar Tarayya ta yi fatali da roƙon neman amincewa da ƙudiri kan batun ɗaliban sakandare su rubuta jarawabar NECO, da WAEC da Kuma JAMB kyauta na zangon shekarar 2023/2024.
An nemi a yi wa iyayen yara  afuwar biyan kuɗin jarabawar ne ,saboda a rage masu raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da ita, tun bayan cire tallafin fetur.
Ɗan Majalisa Anamero Dekeri, na Jam iyyar APC daga Jihar Edo ne ya bijiro da wannan roƙon, inda ya roƙi Majalisar Tarayya da ta umarci Gwamnatin Tarayya ta biya wa kowane ɗalibi kuɗin jarabawar WAEC, NECO da UTME.
Sai dai kuma an yi fatali da buƙatarta Ɗan Majalisar, bayan an yi doguwar mahawara a Zauren Majalisa.
Dekeri ya ce shi dai da zuciya ɗaya ya nemi a yi wa iyayen ɗalibai wannan sassauci, saboda irin halin ƙuncin da suka shiga, tun bayan cire tallafin fetur.
Ya ce ce kuɗin da talakawa ke kashewa kan fetur da tsadar zirga-zirga ya na yi wa ɗan abin da suke samu a yau da kullum babban giɓi.
Ya Kara da cewa tunda Gwamnatin Tarayya ta tara rarar ɗimbin kuɗaɗe bayan cire tallafin fetur, to kamata ya y,i ta yi wa iyayen ɗaliban da ke fita daga matakin karatu na sakandare sassauci, ta bar rubuta jarabawar 2023/2024 su rubuta kyauta, ba tare da biyan ko sisi ba.
“A kullum tun da aka cire tallafin fetur, gwamnatin tarayya na ajiye tarar naira biliyan 17.2 a kowace rana.”
Kan haka ne ya yi roƙon cewa Ma’aikatar Ilmi ta Tarayya ta yi shelar yi wa iyayen ɗalibai sassaucin kada su biya kuɗaɗen jarabawar ta  NECO, da  WAEC da Kuma UTME.
An yi ta ja-in-ja, daga ƙarshe Kakakin Majalisar Tarayya, Abbas Tajudeen ya bada fili a yi zaɓe,kamar yadda Al adar zauren take . Sai dai  waɗanda ba su so a yafe wa iyayen yara kuɗaɗen ne su ka yi nasara.
Hafsat Ibrahim