INGANCIN MANJA GA JIKUNAN MU

0
281

Amfanin man ja ga jikin dan Adam.

Ana cire man ja ne daga kwakwan man ja, ana iya amfanin da ita wajen girke- girke don kuwa ba ta da sinadarin cholesterol.

A gargajiyaance, Ana amfani da man ja wurin maganin shidewa ga kananan yara.

Man ja na boye shekaru ga mai amfani da ita, sakamakon kunsar vitamins E da A da tayi . Tana kashe wasu alamun tsufa da za su iya nuna wa jiki.

Manja na sa tsayin gashin Kai,kuma yana ba da matukar mamaki tare da hana zubewanrsa, yana Kara karfin gashi tare da walkiyarsa.

Man ja na tausasa fata da hana tsufa da

daidaita ta karfin jini. bincike ya nuna cewa man ja na ingannta sassan jikin dan Adam.

Man ja na maganin warin jiki,sakamakon kamshinta Mai karfi idan kana shafata akai akai a jiki.

 

Daga Zainab Sani Suleiman.