YADDA AKE HADA LEMUN AYABA NA BANANA SMOOTHIE

0
822

Wannan lemun ana hadashi da ayaba ne kuma yana da daddi ga kuma kyau wajan gyara mana fata da kuma lafiyar jikin mu. Ayaba ta na daya daga cikin kayan itatuwa da aka fi amfani da su a duniyar nan saboda wasu kwararan dalilai. Cin ayaba yana rage hawan jini da kuma bayar da kariya ga cututtukan daji da na asma. Yadda ake samun karuwar amfani da ayaba a duniya, tambayoyin da mutane su ke yi akan fa’idar ayaba ba ya bayar da wani mamaki.

ABUBUWAN BUKATA SUNE

  • Ayaba
  • Greek yoghurt ko madaran ruwa
  • Vanilla flavor

YADDA AKE HADAWA

  1. Zamu bare ayaban mu da yayyi kankara mu sa acikin blende in mu sai mu zuba yoghurt ko madaran ruwan .
  2. Idan muna so zamu iya amfani da youghurt da kuma madaran ruwan mu sai mu sa vailla flavor muyi nika a blender in mu. 
  3. Mu tabbatar mu nika haddin mu ya niku sosai toh banana smoothie inmu ya hadu.
  4. Ga saukin hadawa, gashi baya bukata kaya da yawa, ga daddi.

 

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here