MATSALAR WARIN BAKI DA HANYOYIN DA ZA’A MAGANCE SHI

0
526

Sakamakon yawwan koke da kuma matsala da ake samu kan warin baki likitocin Nigeria da sauran kwarrarru sun fara wayar da kan al’umma a kan hanyoyin da zaabi wajen kauce kamuwa da wannan matsala da wasu ke fiskanta harma ya kai ga tsangwama garesu.

Tsaftan baki yanada muhimmanci domin kuwa idan anyi kwalliya bai kamata ana mantawa da tsaftace baki ba sabida duk yadda mutum yakai ga caba kwalliya ko ado in har yayi magana akaji wari a bakinsa toh duk wannan kwalliya toh fah bazaiyi daraja a fiskan wasu ba.

Larurar warin baki babban matsala ne da ya kamata mutane su maida hankali wajen kaucewa kamuwa da ita. Haka zalika sau da yawa matsalar warin baki na lalata zaman aure wanda har yake iya kaiwa ga saki sabida yadda daya daga cikin ma’aurata ke kasa hakuri da juna kan larurar warin baki.

Warin baki ya samo asali ne a lokacinda kake cin abinci kananan abinci suna kama cikin hakori a lokacin da abinci ya makale sai kwayoyin cuta akan wadannan abincin. Kula da lafiyan hakora shine abu mafi muhimmanci da zaayi wajen ganin an kauracewa warin baki.

Rashin kula da tsabtar baki shine babban musabbabin abunda ke janyo matsalar warin baki, haka zalika rashin kwakwale sauran abinci dake makalewa a lokacin cin abinci. Sannan kuma idan ana sake da hakorin roba yanada kyau a rika wanke su sannan a ciresu a baki lokacin da zaa kwanta bacci.

Haka zalika yawaita shan ruwa nada amfani domin yana wanke duk wani datti da yake makale a baki, sannan idan zaa kwanta bacci ana wanke baki haka zalika a lokaci da aka tashi bacci a wanke domin yana matukar rage warin baki ga Masu larurar.

Hakazalika mutane da yawa sunyi imani cewa ruwan Abarba shine mafi inganci wurin saka baki yayi kamshi duk da cewa babu wani hujja a kimmiyance, sa’nnan wanke baki da ruwan soda yanada amfani wajen magance warin baki domin yana kashe duk wani bacteria dake kawo wannan cutan, zaka iya zuba cokali 2 na garin soda a cikin ruwan dumi sai ana kurkure baki dashi. Haka zalika wasu masana kiwon lafiya sunyi itifaki kan cewa  yawaita cin kanumfari yana magance kwayoyin cututtuka dake haifar da warin baki. 

Abu na karshe dake jawo matsala na warin baki shine rashin canja brush a koda yaushe,zakaga wasu sai suyi wata da watanni suna amfani da brush din wanke hakori daya wanda a Harkar lafiya ba’aso kana amfani da brush daya har ya kai na wata 1 ma anfi so a yawaita canja shi haka zalika da zaran ya fadi a kasa toh bai kamata ka maidashi baki ba sai dai kasa a ruwan zafi ya kashe duk wani kwayan cuta na ciki ko kuma ka canza sabo.

Idan har ka kiyaye duk waennan abubuwa da na lissafo amma warin baki bai tafi ba toh ka tuntubi likita ko likitan hakor.Allah yasa mu dace.

BY:UMMU KHULTHUM ABDULKADIR