YADDA AKE HADA DAMBUN KAZA { CHICKEN FLOSS}

0
3571

Dambun kaza wanni hanya ne na sarafa kazan mu, ta yadda zamu ji daddin ta. Ayau zamu koya maku yadda ake hadda wannan dambun kazan mai daddi kuma mai auki.

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

* Kaji

* Tattasai

* tarugu

* Albasa da tafarnuwa

* Oil

* Kanunfari

* Masoro

* Citta

* Thyme

* Curry

* Kimba

* Nutmeg

* Cinnamon

* Maggi

* gishiri

YADDA AKE HADAWA:

  1. Da farko zamu wanke kaza da kyau a zuba a tukunya, sai a zuba ruwa yanda kazar zata dahu luguf kuma ruwan ya tsotse a jikinta.
  2. Sai mu zuba dakakkan sinadaran kamshi dana dandano, tare da maggi da gishiri. Sai a barta tayi ta nuna.
  3. Bayan kazan ya nuna sai ki sauke, ki samu abun da zaki tuqa dashi, sai ki yi ta farfasa kazan kina tuqe shi tare da cire qasusuwan, idan kina tuqewa zaki ga ya koma babu wani naman da bai fashe ya koma kamar niqaqqen nama ba.
  4. In kuma baki son wahala sai ki samu  turmi mai kyau kiyi ta juyawa a ciki, wasu kuma a blender  suke nika namansu kowa da yadda yake nika ko daka nashi. Saboda so ake ya tuqu ya zama babu salen naman.
  5. Idan kin gama sai ki ďandana maggi da sauran spices idan basu fito ba yanda kike so sai ki dan kara. Amma kadan saboda idan naman ya soyu maggin zai fito dayawa.
  6. Sai ki jajjaga kayan miyanki dan dai-dai tare da tafarnuwa ki zuba a kai a juya ya hade. Sai ki daura non stick pot a wuta ki zuba mai a bar shi yayi zafi amma ba sosai ba, sai a dibo kajin a zuba a cigaba da juyawa har sai yayi golden brown. Zaki iya yi kina qara mai amma a kula saboda kada yayi yawa ana ci ana tatse mai.
  7. Daga nan sai ki juye a tray, idan akwai ragowar sai ki sake zuba mai sannan ki sake zubawa. In an gama duka sai ki zauna ki sake rage duk wani abun da baki so da ragowar kananun kasusuwa da baza a rasa ba.

 

  1. Abun Lura game da Dambu kaza mai Kaman auduga shine ya danganta da yanayin tukawan kazan ki kafin ki fara soya shi domin kuwa yawan tukawan ki yanayin yadda dambun ki zai kasance.

 

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho