Ministan Buhari mai shekaru 74 ya auri budurwa mai shekaru 18

0
387

 

Ministan aikin noma da raya karkakara, watto Sabo Nanono ya auri  yarinya mai shekaru 18 a  ɗaurin auren da aka yi cikin sirri kamar yadda muka samu rahoto daga Daily Nigerian. Nanono, mai shekaru 74 ya auri kyakkyawar yarinyar a auren sirri da mutum uku daga danginsa kadai suka hallarci ɗaurin auren da aka yi a Jere a jihar Kaduna. “Mutane uku kawai ministan ya wakilta kuma ya gargaɗe su da kada su bayyana wa mutane cewa ya yi aure,” a cewar wani majiya daga iyalin da ya nemi a boye sunansa. Haka zalika Daily Nigerian ta gano cewa tuni amaryar ta tare a gidan Ministan da ke Tarmandu Close a Kano. Duk da cewa iyalan ministan ba su yarda auri yarinyar da ya girma da shekaru 50 ba, majiyoyi sun ce ya tsaya kan bakansa sai da aka yi auren. “Ministan ya tsunduma kogin soyayya. Bisa dukkan alamu babu abin da zai sauya masa ra’ayi,” a cewar majiyar.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho